Shegen gora: An cafke wani mai sana'ar wanki da guga da laifin saida kayan mutane
Jami'in dan sandan Najeriya a garin Abuja a ranar Juma'a ya gurfanar da wani mai sana'ar wanki da guga mai suna Benjamin Ayuba dake da shekaru 29 a duniya a gaban kuliya bisa zargin saida kayan jama'a da suka kawo masa wanki.
Dan sandan dai mai suna John Okpa da ya kai shi kara a kotun ya zarge shi ne da laifin zamba cikin aminci da kuma rashin gaskiya.
KU KARANTA: Sanatan PDP yayi tsokaci game da batun komawar sa APC
Legit.ng ta samu cewa tun farko dai wani jami'in hukumar tsaron farin kaya ne dai mai suna Abubakar Abdullahi ya kai mai wanki kara inda yace ya sayar masa da kayan da suka kai darajar Naira dubu 119.
A wani labarin kuma, Akalla mahajjata takwas ne kamar yadda muka samu daga majiyar ta kamfanin dillacin labarai da suka fito daga jihar Kebbi dake a Arewa maso yammacin Najeriya sukayi kicibis da 'yan damfara a kasar Saudiyya.
Haka zalika kamar yadda muka samu, 'yan damfarar sun yiwa mahajjatan wayau inda har suka samu nasarar kwace masu dukkan kudaden guzurin su sannan suka yi layar zana.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng