Wasu mahajjata 8 daga Arewa sunyi kicibis da 'yan damfara a kasa mai tsarki

Wasu mahajjata 8 daga Arewa sunyi kicibis da 'yan damfara a kasa mai tsarki

Akalla mahajjata takwas ne kamar yadda muka samu daga majiyar ta kamfanin dillacin labarai da suka fito daga jihar Kebbi dake a Arewa maso yammacin Najeriya sukayi kicibis da 'yan damfara a kasar Saudiyya.

Haka zalika kamar yadda muka samu, 'yan damfarar sun yiwa mahajjatan wayau inda har suka samu nasarar kwace masu dukkan kudaden guzurin su sannan suka yi layar zana.

Wasu mahajjata 8 daga Arewa sunyi kicibis da 'yan damfara a kasa mai tsarki
Wasu mahajjata 8 daga Arewa sunyi kicibis da 'yan damfara a kasa mai tsarki

KU KARANTA: Malamin addini yayi hasashen wanda zai lashe zaben 2019

Legit.ng ta samu cewa shugaban mahajjatan daga jihar Kebbi, Alhaji Abubakar Argungu shine ya tabbatar da faruwar lamarin sannan kuma ya shawarci sauran mahajjatan da suyi taka-tsantsan.

A hannu daya kuma, Labarin da muke samu daga majiyoyin mu sun tabbatar mana da cewa ba da dadewa ne ba dai waji jirgi mai saukar angulu kirar helikwafta ya rikito da mutum tara a cikin sa a wasu tsaunuka dake can a kasar Japan.

Hotunan farko farko dai da wata tashar yada labaran kasar ta fitar sun nuna buraguzan jirgin a cikin itace a garin Gunma dake a arewa maso yammacin garin Tokyo, babban birnin kasar.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng