Zaben 2019: Wani malamin addini ya yi hasashen wanda zai lashe zaben shugaban kasa
Wani babban malamin addinin kirista dan asalin Najeriya dake zaune a kasar Afrika Ta Kudu mai suna Samuel Akinbodunse ya rikirkita dandalin sadarwar zamani biyo bayan wani hasashe da yayi na wanda zai lashe zaben 2019 a Najeriya.
Fasto Samuel Akinbodunse din dai da ke zaman shugaban rukunin majami'un Freedom for All Nation Outreach ya yi ikirarin cewa ubangijin sa ne ya nuna masa wanda zai lashe zaben.
KU KARANTA: Yadda firar Osinbajo da Buhari ta kasance kafin korar Lawal Daura
Legit.ng dai ta samu cewa hasashen nasa kamar dai yadda muka ji daga majiyar mu shine wai matashi ne zai lashe zaben kuma farkon sunan sa ya fara ne da harafin 'S'.
Wani ma'abocin anfani da kafar sadarwar zamanin ta Twitter mai suna Wale Gates ne ya fara yada faifan bidiyon faston lokacin da yake yiwa mabiyan sa wannan jawabin.
Tuni dai 'yan Najeriya suka yi ta tofa albarkacin bakin su game da wannan hasashen musamman ma da yake kawo yanzu masu neman kujerar shugabancin kasar da sunan su ya fara da 'S' Saraki ne kawai sai kuma mai kamfanin jaridar nan ta Sahara Reporters - Sowore.
Ga ma dai faifan bidiyon nan:
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng