Da duminsa: Jami’an EFCC sun kai mamaya gidan tsohon shugaban hukumar SSS

Da duminsa: Jami’an EFCC sun kai mamaya gidan tsohon shugaban hukumar SSS

- Ashe har yanzu EFCC bata manta da maganar tsohon shugaban SSS ba

- Maganar da ake yanzu haka ta kai sumame gidansa dake Abuja

Hukumar yaki da masu cin hanci da rashawa ta kasa EFCC ta kai sumame gidan tsohon shugaban hukumar jami'an tsaro na farin kaya SSS.

Da duminsa: Jami’an EFCC sun kai mamaya gidan tsohon shugaban hukumar SSS a Abuja

Da duminsa: Jami’an EFCC sun kai mamaya gidan tsohon shugaban hukumar SSS a Abuja

Jami'an hukumar sun isa gidan tsohon shugaban hukumar ne Mista Ita Ekpeyong da yammacin yau Alhamis, wanda ake tsammanin an turo su ne bisa umarnin mukaddashin shugaban kasa Yemi Oeinbajo.

Mista Ekpeyond ya jagorancin hukumar tun daga shekara ta 2010 zuwa shekara ta 2015 kafin shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sauke shi tare da nada Lawan Daura, wanda shi ma aka tunbuke shi a cikin satin nan.

KU KARANTA: Tun kafin ai nisa EFCC ta fara bincikar Fayose da matarsa

Daga cikin kadarorin da ake kokarin yin bincike akansu akwai wani gida dake Asokoro a Abuja. A shekara ta 2017 an yi yunkurin yin hakan amma har ta kai ga sabani tsakanin jami'an hukumar farin kayan da kuma jami'an hukumar EFCC, kafin daga bisani Lawan Daura ya shiga cikin maganar tare da hana aikata hakan.

Hukumar tana zargin Mista Ekpeyond akan siyan wasu makamai ba bisa ka'ida ba tare da karkatar da akalar wasu kudin makamai wadanda aka cire domin yaki da ‘yan tada kayar baya na Boko Haram.

Sai dai ya zuwa yanzu babu wanda zai iya bayyana cewa wannan sumame da hukumar EFCC ta kai yana da nasaba da cigaba da wancan zargi da ake masa tun shekara ta 2017.

Mai magana da yawun hukumar ta EFCC Wilson Uwujaren baya daga kira balle majiyarmu ta ji ta bakinsa game da lamarin, amma duk da haka an aike masa da sakon kar ta kwana ko in anyi sa’a ya biyo baya.

Latsawannandominsamunsabuwarmanhajarlabarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmunadandalinsadazumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idankuna da watashawarakobukatarbamulabari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel