Magu ya shiga tsaka mai wuya, ya kai kara ga babban mai shari’a na kasa baki daya
- Zargin shigar da son rai yayin gudanar da shari’ar karar Magu da aka kai gaban alkaliya Binta Nyako wadda yake tuhumar mijinta da ‘Danta’ ya sanya shugaban hukumar EFCC neman a sauya masa alkali
- Tun farko dai an kai Magun kara ne kotu don kin amincewa da nada shi a matsayin cikakken shugaban hukamar EFCC
Mai rikon mukamin shugaban hukumar EFCC Ibrahim Magu ya bukaci babban alkalin kotun daukaka kara Adamu Abdul-Kafarati da ya dauke shari'ar da ake masa akan sukar tabbatar da shi a shugabancin hukumar ta EFCC daga gaban mai shari'a Binta Nyako.
Tun da farko dai ana cajin shugaban hukumar ta EFCC ne da laifuffuka guda 11, wadda mai shari'a Binta Nyako ta ke sauraro.
KU KARANTA: Tun kafin ai nisa EFCC ta fara bincikar Fayose da matarsa
Bukatar sauyin alkalin na kunshe ne cikin wata wasika da lauyan Ibrahim Magu Wahab Shittu ya aike ga babban alkalin, wasikar na dauke da kwanan watan 31 ga watan Yuli.
Ibrahim Magu ya kara da cewa yana kokonton yadda karar da ake kaisa wadda mai shari'a Binta Nyako take saurare zata kasance, tsohon gwamnan jihar Adamawa Murtala Nyako wanda ya kasance miji ne ga ita mai shari'ar ne da kuma ‘Dansa Sanata Abdul'aziz Nyako suna fuskantar tuhuma a EFCC.
Har dai yanzu Ibrahim Magu na a matsayin mai rukon kwarya ne a hukumar ta EFCC sakamakon kin amincewa da majilsa ta yi na tabbatar da shi a matsayin shugaba mai cikakken iko.
Latsawannandominsamunsabuwarmanhajarlabarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmunadandalinsadazumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idankuna da watashawarakobukatarbamulabari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng