Sauya sheka: Wani Sanatan PDP yayi karin haske game da batun komawar sa APC

Sauya sheka: Wani Sanatan PDP yayi karin haske game da batun komawar sa APC

Sanatan dake wakiltar garin Abuja a majalisar dattijai, Sanata Philip Tanimu Aduda ya fito yayi karin haske game da jita-jitar da ke yawo na cewa wai yana shirin ficewa daga PDP ya koma jam'iyyar APC inda yace karya ne.

Sanatan dai ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwar manema labarai da ya fitar a garin na Abuja, inda yace ya kamata mutane su yi kokari wajen rarrabe labaran kanzon kurege da kuma na gaskiya.

Sauya sheka: Wani Sanatan PDP yayi karin haske game da batun komawar sa APC

Sauya sheka: Wani Sanatan PDP yayi karin haske game da batun komawar sa APC

KU KARANTA: Shugaban PDP ya fallasa dalilin da yasa Akpabio ya koma APC

Legit.ng ta samu ya kuma kara da cewa shi da PDP mutu-ka-raba domin kuwa ita kadai ce jam'iyyar da ta ke tabbatar da bin tsarin demokradiyya a tsakanin 'ya'yan ta.

A wani labarin kuma, Shugaban babbar jam'iyyar adawa ta Peoples Democratic Party, PDP Mista Uche Secondus a Najeriya ya ce su fa sun san dukkan dalilan da suka sa tsohon Gwamnan jihar Akwa Ibom, Sanata Godswill Akpabio barin jam'iyyar tasu zuwa APC.

Cif Secondus din dai ko da yake bai bayar da cikakken dalilin sa na fadar hakan ba amma dai ya ce ko kusa komawar ta sa ba ta da alaka da talaka kawai dai don kashin kansa ne yayi hakan.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel