Hajjin bana: An fara gabatar da wa'azi da harshen Hausa a masallacin manzo na Madina

Hajjin bana: An fara gabatar da wa'azi da harshen Hausa a masallacin manzo na Madina

Kamar yadda muka samu daga majiyoyin mu da dama dai, mahukunta a daular musulunci ta kasar Saudiyya sun bayar da amincewar su ga wasu malamai bakaken fata Hausawa su rika yin wa'azi tare da karantarwa da Hausa a masallacin Manzon Allah SAW dake a garin madina.

Mun samu cewa hakan dai nada nasaba ne da yawan Hausawan da suka samu halartar kasar domin yin aikin hajji da kuma aka fahimci suna bukatar karin fadakarwa da karantarwa akan ibadar ta aikin hajji.

A karon farko: An fara gabatar da wa'azi da harshen Hausa a masallacin manzo na Madina

A karon farko: An fara gabatar da wa'azi da harshen Hausa a masallacin manzo na Madina

KU KARANTA: An kama sojan Amurka a Najeriya ya tafka ta'asa

Legit.ng ta samu cewa Sheikh Magaji Ishaq Zarewa ne dai da ya fito daga jihar Kano mahukuntan kasar suka lamuncewa ya rika yin wa'azin.

A wani labarin kuma, Da yawa daga cikin mabiya mazhabar shi'a almajiran Zakzaky a Najeriya sun yi ta nuna jin dadin su game da samun labarin korar shugaban rundunar tsaron farin kaya ta kasa, Lawal Daura da aka yi yau.

'Yan shi'ar dai sun yi ta nuna jin dadin su ne a shafukan sada zumuntar su da ma kuma wasu tituna a wasu garuruwan Najeriya din.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel