Yadda firar Buhari da Osinbajo ta kasance a tarho kafin korar Lawal Daura
A jiya ne dai mukaddashin shugaban kasar Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo ya tsige Lawal Daura daga mukamin sa na shugaban jami'an hukumar tsaro ta farin kaya bayan ya tura jami'an sa sun rufe majalisa.
Sai dai abun da kowa ke fada shine tabbas irin wannan babban mataki, mukaddashin shugaban ba zai iya daukar sa ba ba tare da sanin shi Muhammadu Buhari ba da yanzu haka yake a birnin Landan yana hutu.
KU KARANTA: Yan shi'a sun zazzagar da zallar farincikin su da korar Lawal Daura
Rahotanni dai sun yi ta farda cewa kafin aukuwar hakan, Farfesa Osinbajo ya kira shugaba Muhammadu Buhari ta waya inda kuma suka tattauna batun kafin korar.
Majiyar mu ta APC News Nigeria dai ta tsakuro mana yadda firar tasu ta kasance kafin korar:
Osinbajo: (Bayan gaisuwa) Yallabai zuwan jami'an tsaron farin kaya majalisa fa ban da masaniya akan hakan. Ko kai ka sa shi?
Buhari: A'a ba ni bane. Ba ruwana.
Osinbajo: To bari in tuntubi shugaban nasu inji ko meye dalilin sa na yin hakan.
Buhari: To. Hakan yayi.
Bayan wani dan lokaci;
Osinbajo ya sake kira: Yallabai na kira shugaban nasu amma yana ta yi mani wasa da hankali. Yaki bani hadin kai.
Buhari: To fa! Kayi duk abun da ya dace kawai.
Osinbajo: Na yake shawarar zan kore shi ne saboda a yiwa tufkar hanci.
Buhari: Duk abun da ka yanke yayi dai-dai.
Osinbajo: To na gode.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng