Ta leko ta koma ga ‘yan bautar kasa, ba gaskiya cikin batun karin alawus dinsu zuwa N49,000
- Masu hidimtawa kasa sun ga samu sun ga rashi bayan da akai ta yada jita-jitar kara musu albashi
- Amma sai dai an ce su kara hakuri maganar na nan a mala
Yanzu haka dai hukumar dake kula da masu yiwa kasa hidima ta NYSC ta bayyana matsayinta kan jita-jitar da ake yada na karin alawus din ‘yan bautar kasar daga Naira 49,800 zuwa 49,800.
Tun farko dai shafin Twita mai dauke da sunan APC Newspaper ne ya fara yada labarin karin alawus din, kana mutane suka cigaba da yadawa a shafukan sada zumunta, wanda hakan ya haifar da jin dadi da mabambantan ra’ayoyi.
Amma sai dai rashin jin labarin daga majiya mai tushe ya sanya kokonton a zukatan jama’a da dama, musamman matasan masu shirin fara hidimtawa kasar nan gaba.
KU KARANTA: Boko dadi: Wanda yai kowa cin jarrabawar JAMB a Najeriya ya sami N5m daga gwamnan Borno
A cikin wani jawabi da shafin hukumar ta NYSC ya wallafa a matsayin amsa ga tambayar sahihancin labarin karin albashin da ake yadawa, hukumar ta bayyana cewa dama “Tun da jita-jita ne zancen, ai ba gaskiya a cikinsa”.
Wannan amsa mai kama da martani da hukumar ta bayar a shafinta na Twita ya sanya kurar tararrabin ta lafa.
Amma sai dai shugaban hukumar Brig. Gen. Suleiman Kazaure, a kwanan baya ya bayyana cewa, tuni gwamnatin tarayya ta fara bitar alawus din da ake biyan ‘yan bautar kasar. Kazaure ya bayyana a ranar 2 ga watan Agustan da muke ciki yayin wata ziyarar aiki da ya kai sansanin horas da masu yiwa kasa hidima dake birnin tarayya Abuja.
Latsawannandominsamunsabuwarmanhajarlabarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmunadandalinsadazumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idankuna da watashawarakobukatarbamulabari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng