Abubuwa 10 da Saraki ya fada yayin taron Duniya da suka gudanar yau
- Maganganun masu ruwa da tsaki na cigaba da fitowa tun bayan hatsaniyar da ta afku a zauren majalisar kasa jiya
- Kamar yadda aka tsara jiya, shugaban majalisar dattawan Abubakar Bukola Saraki ya gudanar da jawabinsa ga Duniya
- A cikin jawabin nasa na yau ya ambaci wasu abubuwa 10 da ya kamata ku sani
A jawabin da ya yiwa manema labarai ranar Laraba bayan hatsaniyar da aka samu a majalisar dokokin Najeriya ranar Talata, Bukola Saraki ya ce zabar shi aka yi kafin ya samu kujerar, ba nada shi aka yi ba.
Ya kuma bayyana wasu abubuwa guda 10 masu ban sha'awa, wadanda su ka hadar da:
1. Masu yunkurin tsige shi ne suka kulla kitimurmurar wadda ta saba doka.
2 Yadda al'ummar kasar nan suka nuna juyayinsu akan abin da ya faru jiya, ya tabbatar da cewa basa goyon bayan kokarin tursasawa ko karfakarfa.
KU KARANTA: Dalilan da suka sanya PDP baiwa Saraki mukamin uban-tafiya-jagaba
3. Majalisar kasa gaba take da kowacce ma'aikata a kasar nan, domin ita ce ke wakiltar al'ummar kasar nan baki daya.
4 . Al'umma ne suka zabe mu, don haka al'ummar kasar nan mu ke wakilta, yin karfa-karfa a kanmu dai dai-dai yake da danniya ga ‘yan Najeriya.
5 . Mukaddashin Shugaban kasa Farfesa Yemi Osibanjo yayi namiji kokari.
6 . Kokarin magance yunkurin batawa majalisar kasa suna ko katsalandan ba shi ne abin tambaya ba, alhakin gwamnati ne tun farko wajen magance faruwar hakan, don haka ita zamu zarga idan wani ya faru na rashin dai-dai.
7 . Al'amarin an kitsa shi ne tun watannin da suka shude daga wasu masu Ido da kwalli, amma ba su samu nasarar abin da su ka kudurta ba duk da an kyale faruwarshi.
8 . Majalisar kasa ba ta da bukatar wasu jami'an tsaro wadanda ba na majalisa ba.
9 .An zabe ni a ne matsayin Shugaban majalisar dattawa, kamar yadda kundin tsarin mulkin kasar nan ya baiwa mambobin majalisar dattawa ikon zaben shugabansu.
10. Yau rana ce da zamu tattauna batutuwan da suka shafi Dimukaradiyya ba rana ce da za’ai maganar kudurina na takarar Shugabancin kasa ba.
Latsawannandominsamunsabuwarmanhajarlabarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmunadandalinsadazumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idankuna da watashawarakobukatarbamulabari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng