'Yan shi'a sun bayyana farin cikin su da korar shugaban rundunar tsaron farin kaya, Lawal Daura
Da yawa daga cikin mabiya mazhabar shi'a almajiran Zakzaky a Najeriya sun yi ta nuna jin dadin su game da samun labarin korar shugaban rundunar tsaron farin kaya ta kasa, Lawal Daura da aka yi yau.
'Yan shi'ar dai sun yi ta nuna jin dadin su ne a shafukan sada zumuntar su da ma kuma wasu tituna a wasu garuruwan Najeriya din.
KU KARANTA: 'Yan Arewa 3 sun nuna bajinta a Nahiyar Afrika
Legit.ng dai ta samu cewa hakan baya rasa nasaba da cigaba da tsare jagoran su da rundunar ke yi kimanin sama da shekaru biyu kenan tun bayan hatsaniyar da ta faru tsakanin 'yan shi'a da jami'an sojojin Najeriya a Zariya, jihar Kaduna.
Shi dai Lawal Daura dan asalin karamar hukumar Daura ce ta jihar Katsina wadda kuma itace karamar hukumar da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya fito shima.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng