Muhimman abubuwa 5 da ya kamata ku sani game da sabon shugaban hukumar DSS

Muhimman abubuwa 5 da ya kamata ku sani game da sabon shugaban hukumar DSS

Labarin da muke samu da dumin sa na nuni ne da cewa Matthew Seiyefa da ke zaman darakta mafi girma a hukumar tsaron farin kaya ta kasa shine ya canji Lawal Daura a matsayin sabon shugaban hukumar biyo bayan tsige shi da akayi.

Shi dai Matthew Seiyefa dan asalin jihar Bayelsa ne kuma ya taba rike babban darakta a makaranta koyon harkokin tsaron tarayyar Najeriya ta Institute of Security Studies (ISS) a turance kafin daga bisani ya koma hedikwatar hukumar a Abuja.

Muhimman abubuwa 5 da ya kamata ku sani game da sabon shugaban hukumar DSS
Muhimman abubuwa 5 da ya kamata ku sani game da sabon shugaban hukumar DSS

KU KARANTA: Jami'ar ADC ta Obasanjo ta rabe gida 2

Mai karatu dai zai iya tuna cewa mukaddashin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya tsige shugaban hukumar tsaro ta sirri, wato DSS, Malam Lawal Daura daga mukaminsa biyo bayan farmakin da jami’an hukumar suka kai majalisar dokokin Najeriya da safiyar ranar Talata 7 ga watan Agusta.

Ga dai wasu muhimman bayanai da ya kamata ku sani game da Matthew Seiyefa:

1. Matthew Seiyefa ya fito ne daga jihar Bayelsa

2. Kafin nadin sa shugaban hukumar DSS, shine babban Darakta a ma'aikatar.

3. Ya taba zama shugaban makarantar koyon harkokin tsaro.

4. Shekarun sa 34 yana aiki a hukumar.

5. Ya taba aiki a jahohin Osun, Akwa Ibom da kuma Legas.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel