Karfin imani: Yadda wasu masallata a Indonesiya sukayi lokacin da girgizar kasa ta riske su a masallaci

Karfin imani: Yadda wasu masallata a Indonesiya sukayi lokacin da girgizar kasa ta riske su a masallaci

Jami'ai dake aikin ceto na cigaba da azama wajen neman mutanen da ake zaton buraguzan kasa sun rufe su a wani masallaci na kasar Indonesiya lokacin da girgizar kasa ta afka masu suna sallah.

Lamarin da ya auku a ranar Lahadin da ta gabata dai masana sun ce girgizar kasa ta kai maki 6.7 kuma kawo yanzu alkaluma sun nuna cewa ta kashe kusan mutum 100 kuma ta sa mutane 20,000 sun rasa matsugunansu.

KU KARANTA: Dalilin da yasa muka tsige Lawal Daura - Osinbajo

Legit.ng ta samu cewa masallacin na daya daga cikin dubban gine-ginen da suka ruguje a arewacin Lombok kuma kawo yanzu majiyar mu tace an samu damar ceto mutum bity daga cikin buraguzan.

Wani da lamarin ya auku yana cikin masallacin kuma ya samu tsira da ransa mai suna Kelana dan shekara 53 ya ce Limaminsu ya gudu ana sallah sai sauran mamu ma suka bi shi.

Kafin nan amma faifan bidiyon da yayi ta yawo a kafafen sadarwar zamani sun nuna yadda limamin da wasu daga cikin mamun suka dake suka kuma cigaba da gudanar da sallar su duk kuwa da girgizawar da masallacin yake yi.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng