'Yan majalisar Kano sun shirya yiwa Ganduje Tutsu, za su koma PDP
- Takarar Ganduje a 2019 na fuskatar barazana a Kano
- Manyan jigogin siyasa a jihar na cigaba da ajiye mukaminsu suna bin tsohon gwamna Kwankwaso
- Tsohon gwamnan jihar Rabiu kwankwaso ya sha alwashin sai ya sanya keyar Ganduje ta lashi kasa, wanda a matakan cika burin nasa ne har ya sauya sheka zuwa PDP
A kalla ‘yan majalisar jihar Kano bakwai da mataimaka gwamnan jihar goma ne suka kammala shirye-shiryen sauya sheka daga jam’iyyar APC zuwa jam’iyyar adawa ta PDP.
Wannan aniya ta su ta sauya sheka ta biyo bayan ajiye aiki da mataimakin gwamnan jihar Farfesa Hafiz Abubakar yayi, wanda shi ma ake kyautata zaton zai bi mai gidansa a siyasa wato tsohon gwamnan jihar Rabiu Musa Kwankwaso.
Farfesa Hafiz dai ya mikawa gwamna Ganduje takardar sauka daga mukaminsa a ranar Lahadi tun gabannin a kai ga tsige shi.
KU KARANTA: Sai da na roki ‘yan majalisar Kano don kada su tsige mataimaki na, amma ya watsa min kasa a ido
Wadannan ‘yan majalisu da suke shirin sauya sheka zuwa PDP ana zaton magoya bayan tsohon gwamna Kwankwaso ne, wanda tuni shi ma ya tsalka katanga zuwa PDP.
Wani mataimakin gwamnan na musamman wanda shi ma tuni ya mika takardar ajiye aikinsa a jiya Litinin, kuma guda daga cikin goman da zasu sauya shekar Barr. Hafiz Ahmed Bichi ne ya tabbatar da shirin nasu ga jaridar The Nation.
Ahmed Bichi ya tabbatar da cewa yanzu haka shirye-shirye sun kammala na komawarsu PDP amma suna cigaba da tattaro kan magoya bayansu don su yashe APC a Kano baki daya sannan su dirga cikin PDP.
Matukar dai aka cigaba da irin wannan sauya sheka da ajiye mukamai a gwamnatin ta Kano tabbas gwamna mai ci Abdullahi Umar Ganduje zai fuskanci matsala babba a yunkurinsa na neman zarcewa.
Latsawannandominsamunsabuwarmanhajarlabarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmunadandalinsadazumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idankuna da watashawarakobukatarbamulabari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng