Kalli hotan kyakkyawan jaririn da aka jefar a bola
- Allah mai iko, wasu na tsananin son samun haihuwa wasu kuma ya basu suna jefarwa
- Wata mata ta ajiye Jaririnta ta arce a Kaduna
- Har ya zuwa yanzu ba'a kaiga gane ko wacece ba
An tsinci wani kyakkyawan jaririn yaron a bayan wani kango daidai da babbar makarantar Sakandire ta Higher Islam dake Tudun Wada Kaduna.
Bayanai sun tabbatar da cewa wata mata ce tazo da cikin mota kirar Golf sannan ta ajiye jaririn kana suka gudu a guje.
KU KARANTA: An ceto wata Jaririya a karkashin Tirela a Kaduna, mahaifiyarsa ce taso kashe shi
Yanzu haka dai an bar ‘yan wadanan unguwa da sallallami da salati, yayinda wasu suke kokarin sanar da hukuma.
Ko da a watan da ya gaba sai da aka kama wata yarinya da take yunkurin kashe jaririnta bayan da ta ajiye shi a karkashin Tirela da zimmar ta tatsile shi.
Haka zalika a cikin dai watan da ya gabata ma a jihar Legas aka wayi gari da ganin wata jaririya da yasar a cikin bola
Shegiyar uwa: Mutan unguwa sun waye gari da ganin sabuwar jaririya cikin bola
Latsawannandominsamunsabuwarmanhajarlabarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmunadandalinsadazumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idankuna da watashawarakobukatarbamulabari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng