Ba za ku iya tsige Saraki ba – Sanata Danbaba
Sanata Ibrahim Abdullahi Danbaba mai wakiltan Sokoto na kudu a majalisar dattawa yace ba zasu taba yin danasanin barin APC zuwa PDP ma kamar yadda ake fadi, yayinda yayi gargadi akan yunkurin tsige shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki.
“Ta yaya zaku tsige shi, ba zaku iya tsige shugaba kamar na majalisar dattawa ba tare da kuna da kaso 2 cikin 3 ba, kuna bukatar sanatoci 73 kafin ku iya tsige shi.”
Ya kara da cewa “Lamarin shine kawai bamu bari mutane suna tafiyar da gwamnati yadda suke so ba, muna bari mutane su tafiyar da gwamnati akan tsari da kundin tsarin mulkin Najeriya ne.”
Da yake martani da kiran da wata kungiya tayi ga gwamnan Sokoto Aminu Tambuwal na yayi murabus saboda ya sauya sheka, yace babu adalcin yin hakan.
KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: An hana magatakardan majalisar dokokin kasar shiga majalisa
Yace ba zai yi murabus ba domin ba APC c eta zabe shi ita kadai ba, mutanen Sokoto ne suka zabe shi.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng