Assha: An kashe wasu Fulani biyu a Filato

Assha: An kashe wasu Fulani biyu a Filato

- Tsugunno bai kare kan matsalar rashin tsaro a jihar Filato

- Bayan lafawar kurar rikicin da ya barce a watan da ya gabata, an sake samun sabon labarin kashe wasu Fulani

- Wadanda aka kashen dai suna kan hanyarsu ne ta tafiya a Mota

Hukumar ‘yan sanda ta jihar Filato ta tabbatar da mutuwar wasu Fulani guda biyu bayan da wasu ‘yan bindiga suka budewa motarsu wuta a yayin da suke tafiya a karamar hukumar Barkin Ladi dake jihar.

An kashe wasu Fulani biyu a Filato

An kashe wasu Fulani biyu a Filato

Kakakin hukumar ‘yan sanda na jihar DSP Tyopev Terna ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce an binne gawar wadanda suka rasun a jiya Litinin sannan ya shaidawa jama'a cewa ana cigaba da bincike domin gano wanda suka aikata danyan aikin.

Sakataren kungiyar Fulani makiyaya ta Miyetti Allah Abubakar Gambo ya tabbatar da faruwar hakan, inda ya shaida cewa suna zargin ‘yan bindigar Berom ne suka aikata wannan aika-aika.

KU KARANTA: Yanzu Yanzu: Jami’an DSS sun mamaye harabar majalisar dokokin kasar (bidiyo)

Ya kara da cewa motar kirar J-5 tana dauke da mutane hudu kuma mutane biyu sun rasa rayukansu, sauran kuma suna asibiti suna cigaba da murmurewa daga raunukan da suka samu.

Gambo ya ce an sanarwa da hukumar ‘yan sanda ta yankin Barkin Ladi domin yin bincike akan lamarin kuma nan take suka tura jami'an su domin ganewa idanunsu.

Ya bayyana sunayen wanda suka rasun a matsayin; Malam Idris Kabir Faya mai shekaru 45 daga kauyen Maitumbi dake Mangu tare da Malam Abdulmudallif mai shekaru 30 a duniya daga yankin Kombun dake Mangua.

Latsawannandominsamunsabuwarmanhajarlabarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmunadandalinsadazumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idankuna da watashawarakobukatarbamulabari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel