Kaico: Sanadin zubda cikin da wani malamin addini yayi mata ta sheka barzahu

Kaico: Sanadin zubda cikin da wani malamin addini yayi mata ta sheka barzahu

- Alakar wani malamin addini da matar wani mutum da yake zaune a kasar waje ta haifar da kwakyariya

- Ya yiwa matar ciki a sandin zubarwa ta sheka lahira

- 'Yan sanda tuni suka damke shi har ma ya fara bayani

Rundunar ‘yan sanda ta kasa reshen jihar Edo ta damke wani Fasto mai suna Ngbeken Elvis dan kimanin shekaru 32 bisa mutuwar wata mata mai suna Mama Sarah, a sakamakon kokarin zubar da cikin da ya yi mata.

Kaico: Wani malamin addini ya zama ajalin wata mata bayan yayi mata ciki
Kaico: Wani malamin addini ya zama ajalin wata mata bayan yayi mata ciki

Elvis wanda malamin addini ne wata Coci da ba'a bayyana sunanta ba, ya fara shiga al'amarin matar ne tun watanni 6 da suka wuce, Inda ya yaudare ta har ya kai ga yi mata ciki.

Matar wacce mijinta yake zaune a kasar waje, amma ita kuma tana zaune a gidan da mijin nata ya gina mata tare da ‘ya’yanta 4 a kauyen Okhokhugbo da ke karamar hukumar Egor din jihar Edo.

Matar ta mutu ne a wani asibiti da aka garzaya da ita domin ceton ranta sakamakon jinin da take zubarwa a lokacin da ta sha maganin da zai zubar mata da cikin da ke jikinta.

Jim kadan da faruwar wannan al'amarin ne jami'an ‘yan sanda suka damke Faston domin dama can ‘yan unguwar suna da masaniyar alakar da ke tsakaninsu.

KU KARANTA: Wani magidanci ya tsere bayan ya banka wa masoyiyar sa da ‘ya’yanta biyu wuta saboda wani sabani

Bayan kama shin ne ya bayyanawa jami'an tsaro cewa ya kulla alaka da ita ne tun daga shekarar 2016, bayan da yayi aure bai samu kwanciyar hankali da matarsa ba.

"Babban dalilin da yasa aka kawo ni wannan kauye a matsayin Malamin Coci shi ne, irin yadda na ke fuskantar tashin hankali daga matata".

"Kuma na hadu da marigayyar ne a lokacin da bata da lafiya, inda na yi mata addu'a, bayan jin dadin addu'ar ne ya sanya tai min alkawarin sakamin da tukwici".

Ya kara da cewa daga nan sai muka fara soyayya da ita, wanda har ta kai na koma gidanta da zama, duk da diyarta ta yi zargin alakar dake tsakaninmu amma sai dai ta tsoratar da ita da korarta daga gidan baki daya.

"Bata sanar da ni tana dauke da juna biyu ba, sai ji nayi katsam ta dauki matakin zubar da cikin wanda hakan yayi sanadiyar rasa ranta". Faston ya shaida.

A karshe ya ce zai roki Ubangiji domin ya gafarta masa wannan mummunan aikin da ya aikata, don yayi nadama matuka.

Latsawannandominsamunsabuwarmanhajarlabarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmunadandalinsadazumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idankuna da watashawarakobukatarbamulabari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng