Kwalara ta barke a Kano mutane 11 sun mutu, 40 na asibiti

Kwalara ta barke a Kano mutane 11 sun mutu, 40 na asibiti

- Cutar amai a gudawa ta bullo a Kano cikin damuna

- Har ta yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama

- Gwamnatin jihar ta yi ta sanarwa a kafafen watsa labari kan matakan kariya daga cutar kafin barkewarta

A kalla kimanin mutane 11 ne suka rasa rayukansu wasu kuma sama da 47 su ke kwance a asibitin a sakamakon barkewar cutar amai da gudawa, a yankin karamar hukumar Bebeji dake jihar Kano.

Kwalara ta barke a Kano mutane 11 sun mutu, 40 na asibiti
Kwalara ta barke a Kano mutane 11 sun mutu, 40 na asibiti

Rahotanni sun bayyana cewa an samu barkewar cutar amai da gudawar ne a kauyukan Hayin Madaci da Kuki da kuma Falli-Sarki dake karamar hukumar ta Bebeji.

Shugaban matasan yankin Ubale Dawud, ya bayyana cewa kimanin mako guda kenan al'ummar kauyukan ke fama da wannan annoba. Ya kara da cewa sun kai rahoton abinda yake faruwa ga hukumomin da abin ya shafa, amma har yanzu suna jiran matakin da zasu dauka.

Wani magidanci mai suna Musa Abdullahi, ya bayyana cewa mutum 11 sun rasu ne a yammacin jiya. Sannan akwai kimanin mutane 47 da suke karbar magani a gida da dakunan shan magani wato Kemis, domin babu wani asibiti a kauyukan da annobar ta afku.

KU KARANTA: Kalli hotunan wata jarumar budurwa da ta damke Macijin da ya sare ta, ta kai shi har gaban likita

“Duk da cewa dan majalisar dokoki mai wakiltar karamar hukumar Bebeji Abubakar Galadima Kuki, shi ma daga wannan yankin ya fito amma mun yi kokarin sanar da shi halin da ake ciki, sai hakan ya ci tura" in ji Ubale Abubakar.

Kwalara ta barke a Kano mutane 11 sun mutu, 40 na asibiti
Kwalara ta barke a Kano mutane 11 sun mutu, 40 na asibiti

Wato Uwa da ta rasa diyarta Malama Habiba Muhammad ta bayyana cewa, a ranar Alhamis da yamma ne, yarinyarta mai suna Fauziyya ta fara amai bayan ta je ta duba makotansu masu fama da larurar. “Mun bata magungunan da mu ka siyo daga kemist amma sai dai rai ya yi halinsa”.

Dagacin yankin Malam Tijjani Abdullahi Kuki ya tabbatar da faruwar al'amarin, inda ya ce sun shirya tsaf domin sanar da hakimin karamar hukumar Bebeji domin daukar matakin da ya dace.

Dukkanin wani kokari da majiyarmu tayi na tuntubar shugaban karamar hukumar Bebeji Ali Namadi Bebeji ya ci tura, sakamakon lambar wayarsa a rufe take.

Sai dai da aka tuntubi kwamishinan lafiya na jihar Kano Dakta Kabiru Ibrahim Getso, ya bayyana cewa an tura ayarin likitoci zuwa yankin domin daukar matakan da su ka dace.

Latsawannandominsamunsabuwarmanhajarlabarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmunadandalinsadazumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idankuna da watashawarakobukatarbamulabari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel