Dandalin Kannywood: Abubuwan ban mamaki 5 da baku sani ba game da Jaruma Hadiza Gabon

Dandalin Kannywood: Abubuwan ban mamaki 5 da baku sani ba game da Jaruma Hadiza Gabon

Ko shakka babu Hadiza Gabon yanzu a iya cewa tana daya daga cikin matan da suka shiga harkar fina-finan Hausa ta masana'antar Kannywood suka kuma yi fice sosai ta yadda ko yanzu kasuwa ta watse, a iya cewa dan koli ya ci riba.

Jarumar dai ta shahara sosai inda ta fito a fina-finai da dama tare da lashe kyaututtuka ba iyaka tun bayan shigowar ta harkar fim shekaru kadan da suka wuce.

Dandalin Kannywood: Abubuwan ban mamaki 5 da baku sani ba game da Jaruma Hadiza Gabon

Dandalin Kannywood: Abubuwan ban mamaki 5 da baku sani ba game da Jaruma Hadiza Gabon

KU KARANTA: Daruruwan yan Kwankwasiyya sun yi mubayi'a ga APC a Jigawa

Haka zalika jarumar saboda kwarewar ta da kuma bajintar ta, hakan ne ma ya sanya ake saka ta cikin jerin fitattun mata a harkar fim din da suka fi karbar kudi kafin su taka rawa a fim din.

Legit.ng ta yi dogon nazari game da jarumar, ga kuma wasu abubuwan ban mamaki da muka tattaro maku game da jarumar:

1. A cikin shekara daya kacal jarumar ta koyi yaren Hausa har ta kware don ta shiga fim.

2. Yanzu haka jarumar na jin yare hudu (4) da suka hada da Hausa, Turanci, Faransanci da kuma Fulatanci.

3. Ta ce ta shiga harkar fim ne don ta samu kudin kafa gidauniyar taimakawa nakasassu wanda tuni ta cika burin na ta.

4. Sabanin da yawa daga cikin 'yan matan fim, Hadiza Gabon ta taba yin fim din turanci.

5. Mahaifin ta dan asalin kasar Gabon ne amma kuma mahaifiyar ta 'yar Najeriya ce.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel