Ana zaton wuta a makera: Wani Gandiroba zai yi kwanan gidan yari

Ana zaton wuta a makera: Wani Gandiroba zai yi kwanan gidan yari

- Mai dokar bacci ya buge da gyangyadi

- Wani ma'aikacin gidan yari ya tsinci kansa a matsayin dan fursina

- Bayan damfarar wani da sunan zai sa ma masa aiki

Wani jami'in aikin gidan yari (Gandiroba) ya gurfana gaban kotu bisa laifin damfara. Adamu Usman shi ne wanda yayi karar Abubakar Jidda Usman a gaban wata kotu dake zamanta a yankin Doma dake jihar Gombe.

Lauyar mai karar Rahina Ibrahim Talle ta gabatar da karar gaban kotu tare da cewa Abubakar ya yaudari wanda take karewa kudi har Naira dubu 250,000 da sunan zai sama masa aiki a hukumar tsaro ta civil defense.

Daurowa take a daure mai daurewa: Alkali ya tisa keyar wani Gandiroba zuwa gidan kurkuku
Daurowa take a daure mai daurewa: Alkali ya tisa keyar wani Gandiroba zuwa gidan kurkuku

Ta kara da cewa takardun yarjejeniyar daukan aiki da Abubakar ya kawowa Adamu an gano na jabu ne bayan da yaje tantancewa domin daukarsa aikin na civil defense.

KU KARANTA: 'Yan sanda a Kano sun bazama neman wadanda su kayi fyade yarinya ga yarinya 'yar shekara 3

Bayan rashin nasara da yayi a wajen tantancewa ne daga bisani Adamu ya bukaci da a ba shi kudinsa tunda dai in ba kira ba abinda zai ci gawayi, nan ne tirka-tirka ta soma.

Abubakar ya amsa cewa tabbas Adamu ya ba shi kudi har Naira dubu 250,000 amma ya musanta zargin da ake cewa ya ba shi takardun bogi.

Alkalin kotun mai shari'a Aminu Haruna ya tambayi Abubakar da yayi wa kotu cikakken bayani akan nawa ake kashewa kafin a samu aiki a hukumar ta Civil defense, sai dai wanda ake karar ya bayyana cewa shi ma bai sani ba.

Daga nan ne mai shari'ar ya umarci da a tisa keyarsa zuwa gidan kaso har sai 9 ga watan Agustan nan domin sake cigaba da sauraren shari'ar.

Latsawannandominsamunsabuwarmanhajarlabarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmunadandalinsadazumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idankuna da watashawarakobukatarbamulabari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng