Yanzu-Yanzu: Shugaban kungiyar masoya Buhari da Osinbajo na kasa yayi murabus, ya fice daga APC
Shugaban kungiyar nan ta masoya shugaba Buhari da kuma Osinbajo watau Buhari/Osinbajo Again (BOA) a turance na kasa baki daya mai suna Alhaji Yahya Hammajulde yayi murabus daga mukamin sa sannan kuma ya fice daga jam'iyyar sa ta APC.
Ita dai kungiyar Buhari/Osinbajo Again (BOA) kamar yadda muka samu, kungiya ce da ke da karfin gaske a yankin Arewa maso gabashin kasar nan da aka kafa domin kare muradu da kuma yiwa Buhari kamfe.
KU KARANTA: Buhari ya bayyana yadda yake ji idan aka kashe wani a Najeriya
Legit.ng ta samu cewa shugaban kungiyar dai bayan ya fice daga APC yanzu shine shugaban jam'iyyar nan ta African Democratic Congress (ADC) a jihar Adamawa.
A wani labarin kuma, Mummunan hatsarin mota ya rutsa da tsohon mataimakin kakakin majalisar jihar Filato dake a yankin Arewa ta tsakiya mai suna Yusuf Gagdi a ranar Asabar din da ta gabata.
Kamar dai yadda muka samu, hatsarin ya auku ne lokacin da motar da ke dauke da dan majalisar tayi taho-mu-gaba da wata motar dauke da wabi babban jami'in rundunar sojin saman Najeriya.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng