Baki-ke-yanka-wuya: Wani matashi ya fallasa yadda suke kashe Hausawa da Fulani a Taraba

Baki-ke-yanka-wuya: Wani matashi ya fallasa yadda suke kashe Hausawa da Fulani a Taraba

A wani irin salo dake zaman tamkar dabawa kai wuka a ciki, wani matashi mai suna Panshak Isaiah ya je a kan shafin sa na dandalin sadarwar zamani na Fezbuk inda ya labarta yadda yace suna kashe Hausawa da Fulani tamkar awaki a jihar Taraba.

Matashin dai ya rubuta cewa "Karshen su yazo yau (watau Hausawa da Fulani), gamu nan muna ta kashe Hausawa da Fulani a garin Kunini kamar awaki".

Baki-ke-yanka-wuya: Wani matashi ya fallasa yadda suke kashe Hausawa da Fulani a Taraba
Baki-ke-yanka-wuya: Wani matashi ya fallasa yadda suke kashe Hausawa da Fulani a Taraba

KU KARANTA: Sabon rikici ya lakume rayuka 3 a jihar Filato

Legit.ng ta samu cewa irin wadannan kalaman na nuna kiyayya na zaman tamkar wasu guma-guman dake rura wutar rikicin kabilanci a yankunan jahohin Arewa ta tsakiya irin su Taraba din.

Tuni dai jama'a da dama da suka ga rubutun na matashin suka yi Allah-wadai da shi tare da jan hankali da kira ga jami'an tsaro da su tabbatar da doka ta hau kan matashin domin hakan ya zama izina ga 'yan baya.

Abun zura ido agani yanzu dai shine ko jami'an tsaro za su farka daga baccin da suke yi domin ganin doka tayi aiki akan matashin da ma sauran masu irin tunani da halayyar sa a ko'ina suke a fadin kasar.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng