Kashe-kashe nan da akeyi na matukar damu na sosai - Shugaba Buhari
Shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari a cikin halin alhini da jimami ya bayyana cewa kashe-kashen da kasar ke fama da su a sassa daban-daban na fafin kasar na matukar damun shi fiye da yadda duk wani zai iya tunani.
Shugaban kasar wanda ya samu wakilcin Sakataren gwamnatin tarayya, Mista Boss Mustapha ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabin sa na babban bako a wajen bikin yaye jami'an sojin kasar da suka kammala kwas din su a kwalegin su dake a garin Abuja.
KU KARANTA: Jahohi 21 da ake sa ran shugaba Buhari ya lashe su a zabe 2019
Legit.ng ta samu cewa haka zalika Mista Boss Mustapha ya ce duk da haka gwamnatin ba zatayi kasa a gwuiwa ba har sai ta kakkabe dukkan burbushin bata gari a ko ina suke a fadin kasar nan.
A wani labarin kuma, Labarin da muke samu daga majiyar mu ta BBC Hausa na nuni ne da cewa wasu da ake zargin 'yan bindiga dadi ne sun harbe wasu Hausawa masu sana'ar canjin kudaden kasar waje a garin Fatakwal, babban birnin jihar Ribas dake a kudu maso kudancin Najeriya.
Kamar dai yadda muka samu wadanda aka kashen din sun hada da Ahmad A. Tukur da Yusuf Zaki da Muhammad Rabi'u da kuma Abubakar Tugga.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng