Abun farin ciki: Rundunar soji ta sada yara da iyayensu shekaru 2 bayan sace su

Abun farin ciki: Rundunar soji ta sada yara da iyayensu shekaru 2 bayan sace su

Rundunar sojin Najeriya ba Birgade 22 da aka tura a Operation Lafiya Dole a jiya sun sada yaran da yan Boko Haram suka sace shekaru biyu da suka shiga tare da iyayensu a kauyen Ngafure a karamar hukumar Dikwa dake jihar Borno.

Rundunar sun ceto yaran maza biyu da mata biyu a yayin kakkaba a kauyen Maima a karamar hukumar Ngala dake jihar.

A wata sanrwa da sa hannun daraktan hulda da jama’a na rundunar, Birgediya janar Texas Chukwu ya kara da cewa an kuma samo alburusai 36 a lokacin aikin.

Abun farin ciki: Rundunar soji ta sada yara da iyayensu shekaru 2 bayan sace su
Abun farin ciki: Rundunar soji ta sada yara da iyayensu shekaru 2 bayan sace su

Ya bayyana cewa yaran da aka ceto suna samun kulawar likitoci a ma’aikatar lafiya na sojoji a yanzu haka.

KU KARANTA KUMA: Sojin sama sun yi amfani da jirgin yaki sun fatattaki barayin shanu a kusa da kauyukan Yanwari da Mashema a Zamfara

Ya yabama kokarin sojojin wajen ceto yaran da yan ta’addan Boko Haram suka sace.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel