Boko Haram: Buratai yayi aman wuta ya gargadi kwamandoji akan gujema yan ta’adda

Boko Haram: Buratai yayi aman wuta ya gargadi kwamandoji akan gujema yan ta’adda

Shugaban hafsan sojin Najeriya, Tukur Buratai ya gargadi kwamandojin rundunar sojin Najeriya kan cewa kada su kuskura su bar gurabensu wajen fuskantar yan ta’addan Boko Haram.

Wannan gargadi na kunshe ne a wata wasika mai kalamai 180 da aka aikewa dukkanin kwamandoji a ko wani mataki, dake gudanar da aiki a guraben da yan ta’addan Boko Haram suka kwashe tsawon shekaru tara suka addaban mutane a yankin arewa maso gabashin Najeriya.

Hakan martani ne kai tsaye da kashe-kashen sojoji da jami’ai da yan ta’addan suka yi a kwanan nan.

Boko Haram: Buratai yayi aman wuta ya gargadi kwamandoji akan gujema yan ta’adda
Boko Haram: Buratai yayi aman wuta ya gargadi kwamandoji akan gujema yan ta’adda

Akalla jami’ai biyu da sojoji 43 aka kashe a hare-haren da Boko Haram ke kaiwa sojoji tsakanin 13 ga watan Yuli da 26 ga watan Yuli, inda hakan ya haifar da dacin rai a zukatan manyan sojoji a kasar.

KU KARANTA KUMA: Shahararren dan takara ne kadai zai iya tsige Buhari - Gwamna Dickson

Wani kakakin rundunar yace ba zai yi sharhi akan wasikar ba amma kwamandoji da sauran sojoji dake filin daga sunce suna kallon hakan a matsayin barazana, abun daukar hankali da damuwa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng