Yanzu-yanzu: Buhari ya isa jihar Bauchi
Rahoton da muke dashi na nuna cewa shugaba Muhammadu Buhari ya tafi jihar Bauchin Yakubu da ranan yau Alhamis, 2 ga watan Agusta 2018.
Shugaba Buhari ya tafi jihar Bauchi ne bayan ganawar da yayi da manyan hafsoshin hukumar sojin Najeriya da kuma shugabannin sauran hukumomin tsaro kan yawaitan kai hare-hare da rashin zaman lafiya a kasar.
Daga nan ya gana da gwamnan jihar Jigawa, Mohammad Badaru da gwamnan jiha Kebbi, Abubakar Atiku Bagudu.
Mai baiwa shugaban kasa shawara kan sabbin kafofin yada labarai, Bashir Ahmed, ya bayyana hakan ne a shafi sada ra'ayi da zumuntarsa na Tuwita .
Shugaba Buhari ya tafi jihar Bauchi ne domin halartan taron yakin neman zaben dan takaran kujeran Sanatan APC na maye gurbin marigayi Ali Wakili na mazabar Bauchi ta kudu.
Za'a gudanar da wannan zabe ne a ranan 11 ga watan Agusta, 2018.
KARANTA WANNAN: An yi hatsarin jirgi a jihar Sokoto
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng