Yanzu Yanzu: Gamayyar jam’iyyun siyasa 39 sun bayyana sakatariya da sunayen kwamitinsu
Sabuwar gamayyar jam’iyyun siyasa 39 ta bayyana sakatariyarta na kasa a Abuja.
Jam’iyyar CUPP ta kansance jam’iyyar hadin gwiwa da ta tara jam’iyyun siyasa 39 ciki harda Peoples Democratic Party, Social Democratic Party da kuma Labour Party.
An kafa sabuwar jam’iyyar ne bisa kudirin kwace mulki daga hannun jam’iyyar All Progressives Congress mai mulki a 2019.
Kwanakin baya ne jam’iyyun suka kulla yarjejeniya domin fitar dad an takara guda da zai tunkari shugaban kasa Muhammadu Buhari a 2019.
KU KARANTA KUMA: Kotun Kaduna ta sanya ranar 4 ga watan Oktoba don yanke hukunci kan belin Zakzaky
Domin fara aiki, jam’iyyar ta CUPP ta kuma samar da wabunda ta ambata da suna mabudin kwamiti.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng