Garin neman gira an rasa ido: Wata budurwa ta sheka barzahu a kokarin zubda ciki
- Kowa yaki sharar masallaci Hausawa suka ce tilas sai yayi ta kasuwa
- Wata matashiya ta rasa ranta garin gujewa kunyar Duniya
- Budurwar dai ta mutu ne sakamakon zubda ciki da ya zo da matsala
Wani likita mai suna Olawake Raji tare da wata ma'aikaciyar jiyya sun shiga hannun hukuma bayan mutuwar wata matashiya mai suna Aminat Otisola yayin zubar mata da ciki.
Kakakin hukumar yan sanda na jihar Ogun DSP Abimbola Oyeyemi, ya bayyana cewa lamarin ya faru ne ranar Alhamis, kuma bincike ya tabbatar cewa likitan tare da ma'aikaciyar sun tafka wannan danyen aiki ne a gidan Aminat Otisola.
KU KARANTA: Abin Al-ajabi: Wata mata ta haifi 'yan biyar rigis cikin damuna
Matashiyar ta rasu ne a daidai lokacin da ake kokarin garzayawa da ita zuwa babban asibitin garin Abeokuta. Yanzu haka dai an tattara dukkanin abubuwanta an damka su ga jami'an tsaro domin cigaba da gudanar da bincike.
Shugaban hukumar ‘yan sandan jihar Ahmed Ilyasu yace masu laifin an tisa keyarsu zuwa Ofishin tuhuma domin tatsar bayanai akan yadda lamarin ya afku.
Ya kara da cewa zubar da ciki haramtacciyar sana'a ce duk wanda hukuma ta kama ba tare da wata shaida da ta bashi ikon yin hakan ba tabbas zai fuskanci hukunci.
Sannan shugaban ya yi kira ga jama'a da su daina rufe idon wajen neman kudi ta kowane irin hali musamman abinda ya shafi harkar lafiya.
Latsawannandominsamunsabuwarmanhajarlabarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmunadandalinsadazumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idankuna da watashawarakobukatarbamulabari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng