An kama barayin da suka kashe tsohuwar Kwamishinar 'Yan sandan jihar Katsina

An kama barayin da suka kashe tsohuwar Kwamishinar 'Yan sandan jihar Katsina

Hukumar 'yan sandan Najeriya ta gabatar da mutane 8 da ake zargin su da kashe tsohuwar Kwamishinar 'yan sanda ta jihar Katsina, Farfesa Halimatu Sadiya Idris

An kama barayin da suka kashe tsohuwar Kwamishinar 'Yan sandan jihar Katsina
An kama barayin da suka kashe tsohuwar Kwamishinar 'Yan sandan jihar Katsina

Hukumar 'yan sandan Najeriya ta gabatar da mutane 8 da ake zargin su da kashe tsohuwar Kwamishinar 'yan sanda ta jihar Katsina, Farfesa Halimatu Sadiya Idris.

Hukumar ta gabatar da mutanen ne a jiya Laraba, inda mai magana da yawun hukumar, DCP Jimoh Moshood ya jagoranci shirin a babbar helkwatar 'yan sanda ta Abuja, ana zargin masu laifin da kashe - kashe da aka yi na kwanan nan, satar mutane, fashi da makami akan babbar hanyar Abuja - Kaduna zuwa Kano.

DUBA WANNAN: Da gangan Saraki ya dinga yiwa jam'iyyar APC zagon kasa - Lai Mohammed

Moshood ya ce suna da hannu a kashe Farfesa Halimatu Sadia Idris, wacce aka kashe ta a ranar 22 ga watan Yulin daya gabata, sannan suna da hannu a fashin da aka yiwa Babban Darakta a fannin aikin gona na jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria, Farfesa Mohammed Khalid Othman, bayan haka kuma suna da hannu a sace wata da aka yi da ita da jaririyar ta 'yar wata bakwai.

Ya ce wadanda ake zargin sun hada, Lawal Tukur wanda yake shine shugaban su, Sulaiman Sani wanda ya bayyana cewar ya kashe mutane hudu da hannun sa; Abubakar Ahmad da kuma Abubakar Adamu.

Sauran sun hada da Yahaya Musa, Rufai Tukur Shehu Audi da Kabiru Bala wadanda suka ce sune suka sace Rahinatu Shehu, Aisha Sani da jaririyar ta 'yar wata bakwai a gidan su dake garin Marraraba Guga a karamar hukumar Giwa.

Hukumar ta kuma bayyana wasu abubuwa da aka samu masu laifin dasu wadanda suka hada da: bindiga mai kirar AK47, kayan sojoji guda uku, wukake, babur, sai kuma wasu kayayyaki da ake tunanin na mutane ne da suka kwace.

Moshood yace domin ganin an kara tabbatar da tsaro da kawo zaman lafiya akan hanyoyin, Babban Sufeton 'Yan Sanda na kasa ya bada umarnin kara tura matakan tsaro da kayan aiki a yankunan da abin ya shafa.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel