Kalli hotunan wata jarumar budurwa da ta damke Macijin da ya sare ta, ta kai shi har gaban likita
- Jarumta ba sai maza ba, wata Budurwa ta yi bajinta
- Budurwar ta damke macijin da ya sare ta har zuwa asibitin da zata ga likita
- Duk da cewa likitan ya bayyana macijin a matsayin maras dafi amma wannan hakika aikin a yaba ne
Wata jarumar mata da macijin ya sare ta ta yi ta maza ta damke shi har zuwa asibiti domin ganin likita.
Matar wacce matashiya ce mai matsakaitan shekaru ta rike macijin ne a hannunta duk da cewa ya sareta, amma hakan bai sa ta sake shi ba har sai da aka dauketa zuwa asibiti.
Babban likitan asibitin da ke lardin Zhejiang a kasar China ya bayyana cewa matar ta nannade hannunta da micijinne har sai da ta je asibitin domin karbar magani.
KU KARANTA: Abin Al-ajabi: Wata mata ta haifi 'yan biyar rigis cikin damuna
Likitan mai suna Huang Shengqiang, ya ce macijin ba mai dafi bane, shi ya sa bai yiwa matar illar da za tai mata lahani ko nakasta ta. Ya kara da cewa yanzu haka dai an bata magani nan take bayan ta je asibitin.
Tun da farko dai an ta daukar hotonun wannan mata a lokacin da ta ke rike da macijin a hannunta, tana zagayawa tsakanin majiyatan da ke kwance a asibitin.
Hukumar asibitin ta bayyana cewa matar mai kimanin shekaru 20 da haihuwa a duniya, ta bayyana musu cewa ta hadu da tsautsayin saran macijin ne a lokacin da ta ke tsaka da neman wayarta da ta neme ta rasa.
Latsawannandominsamunsabuwarmanhajarlabarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmunadandalinsadazumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idankuna da watashawarakobukatarbamulabari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng