Dambarwar siyasa: An yiwa Tinubu, Oshiomhole da Amaechi wankin babban bargo
- Siyasar Najeriya na cigaba da fuskantar yanayin dumama tun bayan kadawar guguwar sauyin sheka
- Wani hamidin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya yiwa jigogin tafiyar Shugaba Buhari gugar zana
Tsohon hadimin tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan Reno Omokri, ya bayyana dalilin da ya sa jagororin Jam'iyyar APC suka ki barin jam'iyyar.
Omokri ya rubuta a shafinsa na Tiwita cewa tsoron kamun da hukumar EFCC za ta yiwa Bola Ahmed Tinubu ba zai taba barinsa ya fice daga Jam'iyyar ba. Haka zalika shi ma Adams Oshiomhole abin da ya ke tsoro kenan.
Ya kara da cewa shi ma Ministan harkokin sufuri Rotimi Amaechi ba zai iya ficewa daga Jam'iyyar ba saboda fargarbar fadawar komawar hukumar ta EFCC.
KU KARANTA: Ka shirya tattara kayanka, zamu tashi kiyamar siyasarka a 2019 – APC ga wani Sanatan Arewa
“Ba don tsoron kamun EFCC ba da Amaechi ya fice daga jam'iyyar APC zuwa jam'iyyar PDP" In ji Omokori.
“Saboda gudun abinda zai je ya dawo ne ya hana Bola Tinubu fita, amma da tuni ya yi fatali da jam'iyyar APC".
Sannan "Tunanin abin da zai faru ga Amaechi da Tinubu, shi ya hana Adams Oshiomhole ficewa daga jam'iyyar APC".
Wadannan maganganu dai na zuwa ne a lokacin da siyasar kasar nan ke cigaba da daukar zafi bayan ficewar shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki daga jam'iyyar APC.
Latsawannandominsamunsabuwarmanhajarlabarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmunadandalinsadazumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idankuna da watashawarakobukatarbamulabari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng