Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari ya dawo daga Togo

Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari ya dawo daga Togo

- Shugaba Buhari ya daow Najeriya daga kasar Togo

- A taron da ya je, an nadashi sabon shugaban ECOWA

- Buhari ya canji Shugaban kasar Togo Faure Gnassingbe

Shugaba Muhammadu Buhari ya sauka babban filin jirgin saman Nnamdi Azikwe da ke birnin tarayya Abuja bayan halartan taron ECOWAS/ECCAS a birnin Lome, kasar Togo.

Rahoto daga NTA ya nuna cewa Shugaba Buhari ya dawo da safen nan.

Shugaba Buhari ya tafi kasar Togo a karshen makon da ya gabata domin halartan taron ECOWAS/ECCAS da aka yi na shekaran nan a kasar Togo.

KU KARANTA: Jam’iyyar APC ta dauki matakan ladabtar da shugaban majalisar dattawa

Daga cikin shawarwarin da aka yanke a taron shine nada shugaban Najeriya a matsayin sabon shugaban gamayyar tattalin arzikin kasashen Afrika ta yamma wato ECOWAS.

Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari ya fito yayi magana bayan nada shi inda ya mika kan sa a kasa da ya ji cewa an nada sa Shugaban Kungiyar ta ECOWAS. Shugaban na Najeriya yayi alkawarin yin bakin kokari domin sauke wannan nauyi mai girma da aka daura masa.

Shugaban Najeriya Buhari ya bayyana cewa zai yi aiki da sauran Shugabannin Kasashen Afrika ta Yamma da kuma Gwamnatin babban Kungiyar ta ECOWAS wajen ganin an samu zaman lafiya da cigaba a fadin Yankin Afrika.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng