Da dumin sa: 'Yan Tijjaniya a jihar Adamawa sun fitar da sanarwa game da 'yan Hakika
Labarin da ke iso mana ba da dadewa ba yana nuni ne da cewa shugabannin darikar Tijjaniyya na jihar Adamawa sun fitar da sanarwa a yau din nan a game da 'yan sabuwar akidar nan ta Hakika ta bulla a jihar inda suka ce sam ba musulmai bane.
Su dai 'yan Hakikar kamar yadda muka samu suna alakanta kansu ne da darikar ta Tijjaniya tare kuma da fadin cewa su ma mabiya Shehu Tijjani ne.
KU KARANTA: Sanatoci 7 sun kammala shirin su na komawa APC
Legit.ng ta samu cewa sai dai a sanarwar da shehunnan Tijjaniyar suka fitar dauke da sa hannun Sheikh Hamidu Moddibo Jailani da aka rabawa manema labarai, sun ce su ba ruwan su da su.
A wani labarin kuma, Tsohon shugaban babban bankin tarayyar Najeriya kuma Sarkin Kano, Alhaji Muhammadu Sanusi ya caccakin gwamnatin tarayyar Najeriya karkashin jagorancin shugaba Buhari da kasar Afrika ta kudu bisa kan kin rattaba hannu akan yarjejeniyar kasuwanci a Nahiyar Afrika.
Sarkin yace abun takaici ne ace kasashen Afrika 44 duka sun sanya hannu a takardar amma Najeriya da Afrika ta Kudu sun kekashe kasa sun kiya inda yace ya kamata a sake zama domin lalubo bakin zaren.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng