Yanzu-yanzu: Gwamnan jihar Kwara ya fita daga jam'iyyar APC

Yanzu-yanzu: Gwamnan jihar Kwara ya fita daga jam'iyyar APC

Mintuna bayan sauya shekan shugaban majalisar dattawa, Sanata Bukola Saraki, daga jam'iyyar All Progressives Congress APC, yaronsa gwamnan jihar Kwara Abdul Fatah Ahmed ya bi sawun maigidansa inda ya sanar da komawarsa jam'iyyar PDP.

Gwamnan jihar Kwaran ya bayyana hakan ne ta mai magana da yawunsa, Muhyiddeen Akorode, da yammacin nan. Ya bayyana cewa ya yanke shawaran sauaya sheka ne bayan jin shawarwarin mutanen jihar.

Jawabin yace: "Bayan shawarwari da daga mutane da kuma shawaran masu ruwa da tsaki a jihar Kwara, gwamnan jihar Kwara, Alhaji Abdulfatah Ahmed, a yau ya sauya sheka zuwa jam'iyyar People’s Democratic Party(PDP) bayan lura da cewa jam'iyyar All Progressive Congress (APC) ba tada amfani ga manufar mutanensa."

Gwamnan jihar ya shiga jam'iyyar APC daga jam'iyyar PDP ne a watan Nuwamban 2013 tare da wasu gwamnonin jam'iyyar guda hudu.

Gwamnonin jihar Ribas, Chibuike Rotimi Amaechi; gwaman jihar Sokoto, Aliyu Magatakarda Wammako; gwamnan jihar Adamawa, Murtala Nyako; da gwamnan jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel