Yanzu Yanzu: Kotu ta dakatar da rantsar da sabon mataimakin gwamnan Imo
Wata babbar kotu a Owerri, babban birnin jihar Imo ta dakatar da rantsar da Mista Calistus Ekenze a matsayin sabon mataimakin gwamnan jihar.
Umurnin kotun na zuwa ne a safiyar ranar Talata yayinda ake dab da rantsar da Mista Ekenze.
Babban alkalin alkalai na jihar, Miletus Nlemadim ya sanar da wadanda suka taru don bikin rantsarwan game da umurnin wadda ya kawo tsaiko ga tsarin.
KU KARANTA KUMA: Bamu da niyan barin jam’iyyar APC – Gwamnonin Adamawa da Niger
A wani lamari na daban, Legit.ng ta rahoto a baya cewa, fadar shugaban kasa ta nesanta Shugaba Muhammad Buhari daga yunkurin da wasu 'yan majalisar dokokin APC marasa rinjaye na jihar Benue ke yi na son tsige Gwamnan Jihar, Smuel Ortom.
Shugaban kasar ya jaddada cewa ba zai goyi bayan duk wani mataki da ya sabawa kundin tsarin mulkin kasa ba.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng