Barin zance: Kotu ta ingiza keyar wani da yayi ikirarin kashe makwabcinsa
- Shan giya bai yi rana ba, ya kai wani saurayi ya baro
- Bayan ya sha yayi mankas ne ya zaro bindigi ya ce zai harbe makwabcin nasa
- Daga karshe da ya tsinki kan shi a kotu ido ya rana fata
A ranar talatar nan ne wata kotu dake zamanta a yankin Karmo a garin Abuja hukuncin watanni biyar a gidan kaso bisa laifin barazanar kashe makocinsa.
Felix Okon dan shekaru 22, wanda yake zaune a kauyen Idudake na Abuja, ya amsa laifukan da ake tuhumarsa har guda biyu, laifin tsoratar da rayuwar mutum da kuma cin mutunci.
"Na amsa laifina, ina rokon wannan kotu mai alfarma da ta yafe min tare da yi min sassauci, ba zan sake aikata wani abu irin wannan ba, wannan ma ya faru ne cikin bacin rai. Ba zan sake shan giya nayi maye ba balle har na wulakanta makwabtana ba".
KU KARANTA: Iyalan Dasuki sun kai ministan shari'a AGF Malami kara
Alkalin kotun Mista Maiwa Inuwa a cikin hukunci da ya yanke ya ba shi zabin tarar Naira 8,000.
Tun farko dai lauyan mai gabatar da kara ta bayyanawa kotun cewa a tsakanin 2 ga watan Fabrairu zuwa 20 ga watan Yuli, Okon ya tsorata Raymond tare da wasu ‘yan uwansa ba tare da sun aikata masa komai ba.
Ta kara da cewa Okon yayi barazanar kashe makocinsa ta hanyar nuna masa bindiga wanda hakan ya sabawa kundin laifuka karkashin sashi na 399 da sashi na 397 na Penal Code.
Amma biyo bayan amsa laifinsa lauyan ya roki kotun ta yi duba karkashin sashi na 112 na kundin laifuka na shekara 2015, domin yi masa sassauci.
Latsawannandominsamunsabuwarmanhajarlabarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmunadandalinsadazumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idankuna da watashawarakobukatarbamulabari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng