Zamu yi yaki dan dawo da Buhari da katunan zabenmu – Gwamna Bagudu
Gwamna Abubakar Atiku Bagudu na jihar Kebbi, yace jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Kebbi a shirye suke don yakar kowa da katunan zabensu don tabbatar da cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dawo kan karagar mulki a 2019.
Yace mutanen jihar sun yarda da sake zabar Buhari a zaben shugabancin kasa mai zuwa saboda jajircewarsa wajen ganin ya dawo da martabar kasar a Najeriya.
Ya bayyana hakan a wata ganawa da hukumar National Orientation Agency (NOA) ta shirya a Birnin Kebbi don masu ruwa da tsakin jam’iyyar kan karban katin zabe na zaben 2019.
KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Gobara ta tashi a babban ofishin Ecobank a Lagas
A halin da ake ciki, Gwamnan jihar Adamawa, Mohammed Bindow, da takwaransa na jihar Niger, Abubakar Bello, sun yi watsi da rade-radin dake yawo cewa suna kokarin sauya sheka daga jam’iyyar APC zuwa PDP.
Gwamnonin sun bayyana matsayarsu a wani zantawa da suka yi da manema labarai a lokuta daban-daban a jihohinsu.
Bindow yayi magana a yayinda yake amsa wata tambaya akan lamarin a lokacin day a dawo Yola, babban birnin jihar bayan wani ziyara da ya kai Abuja a ranar Litinin.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng