Gwamna Ganduje yayi magana akan tsige kakakin Kano

Gwamna Ganduje yayi magana akan tsige kakakin Kano

Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya bayyana chanjin shugabanci da aka samu a majalisar dokokin jihar Kano a matsayin wani tsari na karfafa damokradiyan cikin gida.

“chanjin shugabanci ya nuna yadda Kano a matsayin jiha ta dauki lamarin damokradiyar cikin gida da muhimmanci,” inji shi.

Legit.ng ta rahoto cewa an tsige Abdullahi Ata daga matsayin kakakin majalisar dokokin jihar Kano. Yan majalisan sun kuma zabi Kabiru Rurum, tsohon kakakin majalisar jihar da aka tsige kan zargin rashawa.

2019: Gwamna Ganduje yayi magana akan tsige kakakin Kano

2019: Gwamna Ganduje yayi magana akan tsige kakakin Kano

Ana ganin cewa chanjin shugabancin na da nasaba da gabar dake tsakanin Mista Ganduje da Rabiu Kwankwaso; sannan kuma don tabbatar da cewa mabiya Ganduje ke rike da matsayin kakakin majalisar. Kwankwaso ya sauya sheka zuwa jam’iyyar Peoples Democratic Party kuma yana da kudirin son takarar shugabancin kasa karkashin jam’iyyar.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Tsoffin shugabannin kasa Obasanjo da Jonathan sun yi ganawar sirri

Ganduje yayi Magana ne a ranar Litinin lokacin da sabon kakakin da aka zaba ya kai masa ziyara a gidan gwamnatin jihar Kano.

Ya kuma shawarci sabon shugaban da aka zaba da ya yi aiki da kowa ba tare da wariya ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel