Cakwakiya: 'Yan sandan Najeriya sun kama mai injin buga kudin jabu

Cakwakiya: 'Yan sandan Najeriya sun kama mai injin buga kudin jabu

Jami'an 'yan sandan Najeriya shiyyar jihar Enugu dake a yankin kudu maso gabashin kasar nan sun sanar da samun nasarar cafke wani kasurgumin katon dake bugawa tare da kashe kudaden jabu.

Wanda 'yan sandan suka kama, mai suna Collins Oputa dai sun ce ya shahara ne wajen bugawa tare kuma da rabawa yaran sa kudaden jabun domin su damfari masu sana'a daban-daban.

Cakwakiya: 'Yan sandan Najeriya sun kama mai injin buga kudin jabu
Cakwakiya: 'Yan sandan Najeriya sun kama mai injin buga kudin jabu

KU KARANTA: Musulman Inyamurai sun yi muhimmin kira ga yan uwa

Legit.ng sai dai ta samu cewa Collins din ya alakanta laifin na sa da sharrin shaidan sannan kuma yayi alkawarin ba zai sake aikata laifin ba.

A wani labarin kuma, Ma'aikatar lafiya ta tarayyar tace ta kwace akalla kwalebanin maganin mura dake dauke da sinadarin kodin bayan wani gwaji da hukumar kula da tsafta da ingancin kayayyaki tayi akan su.

Mai magana da yawun ma'aikatar, Boade Akinola itace ta bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ta fitar ta kuma rabawa manema labarai a ranar Lahadin da ta gabata a garin Abuja, babban birnin tarayyar Najeriya.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng