EFCC da Mataimakin Bukola Saraki za su ja labule kan wata badakala
- Zargin mallakar wasu kadarori da mataimakin shugaban majalisar dattijai yayi EFCC ta kai masa goron gayyata
- Gayyatar ta biyo bayan gano kadarorin dake da alaka da shi a ne a kasashen ketare
A gobe ne jami'an EFCC zasu sanya mataimakin Bukola Saraki a majalisar dattijai Ike Ekweremadu gaba domin ya amsa tambayoyi kan wasu kadarori da ake hasashen suna da alaka da shi.
Ana sa ran cewa dai gobe ne da misalin karfe 10:00am na safe Ekweremadu zai kai kansa ofishin hukumar ta EFCC dake Abuja.
Wannan dai shi ne karo na biyu da hukumar take gayyatar Sanatan a cikin mako guda. Wata majiya dai ta bayyana cewa Sanata Ike Ekweremadu ya bukaci a daga masa kafa a sauya masa ranar gayyatar farkon da aka yi masa.
KU KARANTA: Hukumar Kwastam ta kama babbar mota makare da Kodin da motocin alfarma na Naira N1.12bn Wannan ta sa "Muka sake tura masa da wata gayyatar sabuwa, kuma har ya tabbatar da karbarta". Majiyar ta bayyana".
Majiyar ta kara da cewa, "Jami'anmu sun shirya tsaf domin yiwa Sanatan tambayoyi kan kadarorin da akw zargin suna da alaka da shi." EFCC na zargin Sanata Ike Ekweremadu ya mallaki kadarorin ne da kudaden da ake kyautata basu da tsarki.
"Wasu daga cikin kadarorin dai an gano su ne a haɗaɗɗiyar daular larabawa da kasar Amurka. Ana zargin mataimakin shugaban majalisar dattijan ne da kin bayyana wasu daga cikin kadarorin nasa a cikin fam ɗin bayyana kadarorin da ya mallaka." Kamar yadda majiyara ta shaida.
Rahotanni dai sun bayyana cewa hukumar ta EFFC na bincikar wannan batu tun watanni tara da suka gabata amma sai yanzu ta nuna.
Wasu daga cikin manyan kadarorin da suke Dubai sun hada da gidaje masu lamba EGG1/1/114 da EGG1/1/115 Emirates Garden, Apartment DFB/12/B 1204 Park Towers, Flat 3604, MAG214 da Villa No.148, MAEEN1 The Lakes, Emirate Hills. Ragowar sun hada da; Boulevard 3901, da manyan gidaje biyu dake Burij Side Boulevard, The Signature; da dakin Otal din 1903 da kuma mallakar Otal din Downtown.
Sauran da suke kasar Ingila sun kunshi; Gidaje hudu a Varsity Court, Homer Street, WIH 4NW London da kuma 52 Ayleston Avenue, NW6, London.
Latsawannandominsamunsabuwarmanhajarlabarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmunadandalinsadazumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idankuna da watashawarakobukatarbamulabari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng