Ni da Kwankwaso ne jagororin PDP a Kano - Shekarau

Ni da Kwankwaso ne jagororin PDP a Kano - Shekarau

- Tun bayan komawar Kwankwaso PDP sau daya tak aka suka gana da babban jigon jam'iyyar a Kano

- Kuma har ya tabbatar da murnarsa bisa dawowar Sanatan Rabiu Musa Kwankwaso PDP

- Masana siya na ganin zaman manyan gwasaken a jam'iyya guda hadari ne ga gwamna Ganduje

Bayan shafe shekaru ana adawa da juna irin ta siya, yanzu dai kasuwar bukata ta hadu gida guda har ma suna shirin cin abinci a faranti daya.

Ni da Kwankwaso ne jagororin PDP a Kano - Shekarau

Ni da Kwankwaso ne jagororin PDP a Kano - Shekarau

A jiya Asabar ne tsofaffin gwamnonin biyu na Kano suka tattauna da juna tun bayan da Rabiu Musa Kwankwaso ya sauya sheka zuwa tsohuwar jam’iyyarsa ta da wato PDP.

Masu fashin bakin siyasa suna hasashen cewa ganawar tasu na da nasaba da yadda zasu shirya zaren sakar kayar da gwamna mai ci yanzu Dakta Abdullahi Umar Ganduje daga mulki.

A shafin twittar Sanatan an sanya hotunan tsoffin gwamnonin Kanon su biyu da aka dauka bayan ganawar da suka yi a Abuja, inda a shafin aka bayyana cewa suna tattauna yadda za su ciyar da Najeriya gaba.

Malam Ibrahim Shekaru ya shaidawa BBC cewa sun dade suna fatan Allah ya dawo da Kwankwaso cikinsu domin tun farko ya san karshen alewa kasa.

"Duk wani dan siyasa yana son kari ko da mutum daya ne, kuma mu wannan tagomashi ne gare mu."

KU KARANTA: Aiki daban da wasa: Sojoji sunyi wakaci-waka tashi da wasu hatsabiban 'ƴan fashi da makami

"Ana cin zabe da kuri'a daya ana faduwa da kuri'a daya. Mutanen da kwankwanso ya zo da su karuwa ce ga PDP duk da cewa ba duka za su bi shi ba." Shekarau ya bayyan.

Ana dai hasashen cewa auren Mage da Beran siyasar zai ruguje kafin zaben 2019 saboda sabani kan wanda zai jagoranci PDP a jihar, amma sai dai Ibrahim Shekarau ya ce, "Ba wani ne yake nadi ba na jagora, idan tsarin jam'iyya za a bi, yanzu batun wanene jagora duk bai taso ba."

"Kwankwaso yana sahun gaba cikin manyan iyayen jam'iyya, idan mun fahimci juna da shi mun zama iyayen jam'iyya muna tare, kuma kafadarmu daya."

A halin da ake ciki dai tuni jita-jita ta yadu kan cewa Shekarau zai koma inda ya fito wato APC amma yace kowa yayi watsi da rade-raden cewa zai koma APC inda yace jita-jita ce kawai. "Ban taba zancen komawa APC da wani ba."

"Babu wani jami'i na jam'iyyar APC da ya zo min da maganar tayi ko da wasa cewa wai in dawo APC," in ji shi.

Ni da Kwankwaso ne jagororin PDP a Kano - Shekarau

Ni da Kwankwaso ne jagororin PDP a Kano - Shekarau

Da yawan mutane na ganin kulla auren tsoffin gwamnonin na Kano a jam'iyyar adawa, babbar barazana ce ga makomar gwamnan Kano Abdullahi Ganduje na jam’iyyar APC.

Latsawannandominsamunsabuwarmanhajarlabarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmunadandalinsadazumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idankuna da watashawarakobukatarbamulabari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel