Aiki daban da wasa: Sojoji sunyi wakaci-waka tashi da wasu hatsabiban 'ƴan fashi da makami

Aiki daban da wasa: Sojoji sunyi wakaci-waka tashi da wasu hatsabiban 'ƴan fashi da makami

- Karshen wasu 'yan fashi da makami da garkuwa da mutane ya zo

- Wani sumame da Sojoji da 'yan sanda suka yi ne kawo karshensu

Jami'an Sojin kasar nan tare da hadin guiwar jami'an yan sanda, sun cafke wasu yan fashi da makami su hudu a yankin Felele dake Lokoja na jihar Kogi.

Aiki daban da wasa: Sojoji sunyi wakaci-waka tashi da wasu hatsabiban 'ƴan fashi da makami
Aiki daban da wasa: Sojoji sunyi wakaci-waka tashi da wasu hatsabiban 'ƴan fashi da makami

Kakakin sojin ƙasar nan reshen rundunar a jihar Lokoja Captain Nick Ejeh, ya ce an yi nasarar cafke sun ne sanye cikin kakin sojoji.

Ya bayyana masu laifin da suna Japhet Ateam, Saviour Daower, Joseph Usar da kuma Isaac Danold dukkaninsu daga karamar hukumar Guma dake jihar Benue.

Ya kara da cewa yan fashin suna tsaka da aikata fashi da makami lokacin da sojin suka far kuma sun shafe lokaci mai tsawo ana bata-takashi.

Ejeh ya bayyana damuwarsa game da yadda masu aikata laifuka suke amfani da kakin sojoji wajen aikata muggan laifuka sannan ya bayyana cewa wasu daga cikin yan fashin sun samu raunuka yayinda wasu kuma suka sha da kyar.

Aiki daban da wasa: Sojoji sunyi wakaci-waka tashi da wasu hatsabiban 'ƴan fashi da makami
Aiki daban da wasa: Sojoji sunyi wakaci-waka tashi da wasu hatsabiban 'ƴan fashi da makami

KU KARANTA: An kone daya daga cikin 'yan fashin da suka kashe wata kyakykyawar budurwa, duba hoto

Wasu daga cikin makaman da aka kama su da shi sun hada da bindiga kirar AK47, sai akwatin harsashi, tare sauran makamai.

A wani cigaban kuma, jami'an ‘yan sanda sun damke mutum biyu wadanda ake zargi suna da hannu wajen yin garkuwa da mutane akan titin zuwa Okene da Lokoja.

Yayin holar mai magana da yawun hukumar DSP William Aya ya bayyana sunayen wadanda aka kama da; Hammed Saleh wanda aka fi sani da Auta, Obajana da kuma Dulla Danladi wanda dukkaninsu ‘yan kabilar Fulani ne.

"Bayan farmakin da aka kai kan ‘yan babura akan hanyar zuwa Okene da Lokoja wanda yayi sanadiyyar mutuwar direban babbar motar kirar Luxury, hakan yasa hukumar ‘yan sanda karkashin jagorancin DSP Babagana Bukar ta shirya jami'an hana fashi da makami domin ganin an yi nasara wajen cafke wasu daga cikin wadanda ake zargin sun aikata laifin.

"Ya zuwa yanzu ana cigaba da bincike kuma za’a kai su kotu domin amsa laifukan da suka aikata" Aya ya bayyana.

An dai yi holar wadanda ake zargin ne tsakanin jami'an sojoji dana ‘yan sanda a a fadar gwamnatin jihar dake Lokoja, gaban gwamnan jihar Yahaya Bello.

Ana sa jawabin gwamnan Bello ya roki jama'a da su cigaba da bawa jami'an tsaro hadin kai wajen ganin an kawo karshen tashin hankulan da ake fuskanta a jihar.

Latsawannandominsamunsabuwarmanhajarlabarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmunadandalinsadazumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idankuna da watashawarakobukatarbamulabari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng