Ku sadu da Janar Fatima Hemminger, kwamandar farko mace musulma a tarihin kasar Amurka

Ku sadu da Janar Fatima Hemminger, kwamandar farko mace musulma a tarihin kasar Amurka

Yayin da musulunci ke cigaba da mamaya a kusan dukkan lungu da sako na duniya, musulmai a kowane jinsi na cigaba da fitowa fili musamman ma a bangarorin su na rayuwa.

Duk da yadda kafafen yada labarai na yammacin duniya a lokuta da dama ke neman bata sunan musuluncin saboda halayyar wasu 'yan tsiraru, musulmai suna ta yin zarra a fannonin su na sana'a, kasuwanci ko kuma aikin gwamnati.

KU KARANTA: Shugaban kungiyar masoya Buhari yayi murabus

Legit.ng dai ta samu nasarar yin kicibis da wata mace mai kamar maza mai suna Manjo Janar Fatima Hemminger wadda hazikar sojan sama ce a kasar Amurka da da take jagorantar runduna ta 12 dake zaman ta farko da ta taba rike makamin.

Haka ma dai kamar yadda muka samu, itace mace ta farko musulma a tarihin kasar da ta taba zama Manjo Janar a gidan sojan saman Amurka din.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel