Aljannar duniya: Ku zo ku ga hotunan gidan da yafi kowane tsada a Najeriya

Aljannar duniya: Ku zo ku ga hotunan gidan da yafi kowane tsada a Najeriya

Duk da dai abu ne mai matukar wahala iya gano hakikanin gidan da yafi kowane tsada a Najeriya musamman watakila saboda girman ta da kuma yawan mutanen ta, hakan bai hana jama'a yin hasashen hakan ba.

Kamar yadda muka samu a yayin binciken mu a kafofin sadarwar zamani, mun samu cewa kawo yanzu dai gidan da yafi daukar hankali a Najeriyar da har ma ake tunanin cewa shine mafi tsada mallakin wani fitaccen dan kasuwa ne mai suna Okwudili Umenyiora.

Aljannar duniya: Ku zo ku ga hotunan gidan da yafi kowane tsada a Najeriya
Aljannar duniya: Ku zo ku ga hotunan gidan da yafi kowane tsada a Najeriya

KU KARANTA: Jerin sunayen muatne 45 dake harin kujerar Shugaba Buhari a 2019

Legit.ng ta samu cewa dai shi dai gidan yana a unguwar Lekki ce dake a garin Legas kuma ance wai an kashe kusan dalar Amuka miliyan 10 wajen gina shi shekaru da dama da suka wuce.

Gidan dai yana da matukar kyau kuma cike yake da kayan alatun rayuwa kala daban-daban da suka hada da tafkin wanka, manyan na'urori da motocin alfarma da dama.

Haka zalika ance gidan an baza fasahar gaske tundaga wajen zana shi har ya zuwa gina shi.

Ga dai wasu hotunan gidan nan a kasa:

Aljannar duniya: Ku zo ku ga hotunan gidan da yafi kowane tsada a Najeriya
Aljannar duniya: Ku zo ku ga hotunan gidan da yafi kowane tsada a Najeriya

Aljannar duniya: Ku zo ku ga hotunan gidan da yafi kowane tsada a Najeriya
Aljannar duniya: Ku zo ku ga hotunan gidan da yafi kowane tsada a Najeriya

Aljannar duniya: Ku zo ku ga hotunan gidan da yafi kowane tsada a Najeriya
Aljannar duniya: Ku zo ku ga hotunan gidan da yafi kowane tsada a Najeriya

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng