Wani dan APC ya tafka abun kunya a kudu, ya bakunci gidan yari

Wani dan APC ya tafka abun kunya a kudu, ya bakunci gidan yari

Wata kotun majistare dake zaman ta a garin Bayelsa a ranar Juma'ar da ta gabata ne ta tasa keyar wani jigon jam'iyyar APC mai suna Cif Perekeme Kpodo zuwa gidan yari bisa zargin sa da akeyi da yiwa wata mata fyade.

Shi dai Mista Kpodo wanda aka ce fitaccen dan adawar gwamnan jihar ne da manufofin gwamnatin sa tun farko an gurfanar da shi ne a gaban kotun inda aka zarge shi da yin anfani da karfi wajen saduwa da matar.

Wani dan APC ya tafka abun kunya a kudu, ya bakunci gidan yari

Wani dan APC ya tafka abun kunya a kudu, ya bakunci gidan yari

KU KARANTA: Sunayen mutane 45 dake harin kujerar Shugaba Buhari

Legit.ng ta samu cewa sai dai an bayar da belin sa ya zuwa ranar da za'a cigaba da shari'ar kamar yadda lauyan sa ya bukata saboda halin rashin lafiyar sa.

A wani labarin kuma, Babbar jam'iyyar adawa a Najeriya ta PDP ta maida kakkausan raddi ga babban ministan sufuri na tarayyar Najeriya Mista Rotimi Amaechi da yace 'yan Najeriya za su zabi shugaba Buhari a 2019 ko da kuwa yana kwance a gadon asibiti ne.

Sai dai a nata martanin, jam'iyyar ta PDP ta ce yanzu 'yan kasar talakawa sun gane tuni sun dawo daga rakiyar duk wani mai neman shugabanci a kasar idan dai har bai da isassar lafiya.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel