Addinin Allah: Musulmai sun samu yancin cin gashin kansu a kasar Filifins
A wani mataki na samar da dawwamammen zaman lafiya a kasar sa, shugaba Rodrigo Duterte na kasar Filifins ya sanar da baiwa yankin kudancin kasar da ke da mafi rinjayen mabiya addinin musulunci karin ikon cin gashin kai.
Wannan mataki dai kamar yadda muka samu, ana sa ran zai kawo karshen takun sakar dake wanzuwa tsakanin yankin da gwamnatin kasar tare da tabbatar da dawwamammen zaman lafiya.
KU KARANTA: Shugaban masoya Buhari yayi murabus
A wani labarin kuma, Shugaban hukumar jin dadin alhazai a jihar Ebonyi dake a shiyyar kudu maso gabshin Najeriya, Alhaji Abas Egwu ya nuna sha'awar sa game da yadda yace suna bukatar addinin musulunci ya yadu sosai a kudancin kasar.
Kamar yadda muka samu, Alhaji Egwu ya bayyana hakan ne lokacin da yake fira da manema labarai jim kadan tattaunawar sa da babban sakataren kungiyar the Ansar-Ud-Deen, Alhaji Ibrahim Kilani a garin Abakalki.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng