Abin Al-ajabi: Wata mata ta haifi 'yan biyar rigis cikin damuna

Abin Al-ajabi: Wata mata ta haifi 'yan biyar rigis cikin damuna

- Kyautar Allah na da yawa, shi yake bawa wanda yaso a lokacin da yaso

- Matar wani direban tsohon Adaidaita sahu ce ta haifi 'yan biyar rigis

- Sai dai da kyar aka shawo kan mijinta don kar ya arce, kasancewar ba shi da hali

Allah ya albarkaci wata mata mai shekaru 29 a duniya mai suna Mrs. Ndidi Odo da haihuwar 'yan biyar a jihar Anambra. Matar ta haihu ne a asibitin God's mercy dake yankin Obiuno, Otolo-Nnewi.

Yanzu haka dai daruruwan jama'a ne su kayi tururuwa domin taya wannan mata murna da samun wadannan 'ya'ya har guda biyar a lokaci guda.

Abin Al-ajabi: Wata mata ta haifi 'yan biyar rigis cikin damuna
Ma'aikaciyar jiyya na bawa jarirai biyar da aka haifa kulawa

Sai dai mai jegon ta bayyana cewa bata taba tsammanin tana dauke da 'ya'ya har guda biyar a cikinta ba, tace ko a lokacin da take zuwa awon ciki an bayyana mata cewa zata haifi 'yan biyu ne kawai ba wai biyar ba.

Ta bayyana cewa tana da wasu yaran wanda suka hada da mata uku da maza biyu, amma daga bisani daya daga cikin matan ta rasu.

Matar wadda a yanzu haka tana koyon dinki a matsayin sana'ar dogaro da kai tace tana cikin koshin lafiya bayan haihuwar jarirai biyar, sai dai ta bukaci al'umma kawo mata dauki tare da taimako domin basu da halin kula da jariran a cewarta.

Odoemena wanda ma'aikaciyar lafiya ce dake aiki da asibitin God's mercy ta bayyana cewa, a lokacin da matar take zuwa awon ciki, bayanai sun nuna cewa 'yan biyu zata haifa, amma daga baya sai girman cikin ya karu wanda daga nan likita ya bada umarnin yi mata wani sabon awo a nan ne aka gano cewar tana dauke da 'yan uku.

KU KARANTA: Burin Dangote daya da ya rage a duniya na sayen Arsenal ya kusa cika

Mahaifin jariran da aka haifa Mista Abuchi Odo, wanda direban adaidaita sahu ne ya bayyana tashin hankalin da ya tsinci kansa a ciki musamman idan ya tuna da irin nauye-nauyen da suka rataya akansa, wanda har ya yanke hukunci guduwa amma dan uwansa da Prince Justin Brown suka lallashe shi tare da bashi baki.

Duk da haka ya koka inda yace tsohon babur din nasa na adaidaita ba zai iya samar masa da abinda zai ciyar da yara tara ba.

Mista Odo ya yi kira ga gwamnan jiharsu Willie Obiano, Mista Peter Obi, Cletus Ibeto, Dakta Ifeanyi Uba, Sir Louis Onwugbuenu, Dame Virgy Etiaba, Archbishop Godwin Okpala da kuma malamar addini Hilary Okeke tare da wasu manyan mutane das u kawo musu dauki.

Shima daga bangarensa Prince Justin Brown wanda yana daya daga cikin ‘yan uwa da abokan arziki yayi kira ga al'umma wajen ganin sun taimaka musu domin kula da jariran da aka haifa.

Latsawannandominsamunsabuwarmanhajarlabarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmunadandalinsadazumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idankuna da watashawarakobukatarbamulabari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng