Rundunar sojin saman Najeriya ta kera sabbin na'urorin yaki masu ban mamakin gaske (Hotuna)
Babbar makarantar koyon fasaha ta rundunar sojin saman Najeriya watau Air Force Institute of Technology (AFIT) dake a garin Kaduna a ranar Juma'ar da ta gabata ne ta baje kolin wasu sabbin na'urorin da ta kera yayin bikin yaye daliban ta karo na 47.
Kamar dai yadda muka samu, na'urorin da suka baje kolin su sun hada da kananan jiragen yaki marasa matuka da kuma na'urar sarrafa hasken rana zuwa wutar lantarki.
KU KARANTA: Jerin yadda girma da mukamai suke a gidan soja
Legit.ng ta samu cewa sauran abubuwan da suka kera sun hada da wasu irin safurin jiragen yaki masu saukar angulu da za su taimaka wajen kai farmaki ga abokan gaba.
A wajen bikin yaye daliban kuma dai mun samu cewa dalibai 257 ne suka kammala karatun su na digiri da kuma difuloma wadanda suka hada da jami'an sojon saman 102, na sojin kasa 2, na sojin ruwa 3 da kuma farar hula 150.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng