Sojin Najeriya sun cafke babbar mota makare da muggan makamai a jihar Nasarawa
Jami'an rundunar sojin Najeriya da marecen yau ne suka sanar da samun nasarar cafke wata babbar mota kirar bas kamfanin Nissan dauke da mutane 20 da suke zargin 'yan bindiga ne makare da muggan makamai akan hanyar su ta zuwa Abuja daga Nasarawa.
Da jami'an sojin suka tambaye su, wadan da aka kaman sun bayyana cewa su mafarauta ne kuma za su je taron su ne na mafarauta na kasa da yake aukuwa Ranar Asabar, 28 ga watan Yuli.
KU KARANTA: Jerin jami'o'in da suka fi tsada a Najeriya
Legit.ng dai ta samu cewa muggan makaman da aka samu daga wurin nasu sun hada da bindigun gargajiya 17, harsashi 135 da kuma wasu bindigun kirar fistol-fistol guda 2.
Sauran abubuwan da aka samu a wurin su kamar yadda sanarwar da mai magana da yawun rundunar Birgediya Texas Chukwu ya sanyawa hannu sune wuka guda 1, adduna guda 3, kwari da baka guda 1 da kuma layu.
Sanarwar ta cigaba da cewa yanzu haka ana bincike kan wadanda aka kama din kuma da zarar an kammala za'a hannanta su zuwa ga hukumar da ta dace domin shari'a.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng